Tazarar dake tsakanin mai kuɗin duniya na yanzu wato Elon Musk da kuma mai kuɗin Africa baki ɗaya wato Aliko Dangote, ta fi tazarar China zuwa Colorado tsayi 😭.


A Nigeria kuwa, kamar daga Hotoro zuwa Abeokuta ne a ƙafa… babu ruwa babu hutu 😂.
A Africa kuma kamar daga Burkina Faso zuwa Congo ne a keken guragu 😹.
Ni kuma tazarata da Elon Musk kamar daga sama ta 7 ne zuwa ƙasa ta 7 .
Ɗangote da kake ji shine mafi kuɗi a Africa, total Net Worth ɗinsa kusan Billion 36 Dollars ne. Shi kuma Elon Musk yana da sama da Billion 800 Dollars 😭.
Kamar ace kai kana da Naira Miliyan 1, sai wani yana da Naira Miliyan 22 😅.
Kai kuma kana ta jin “ai duk mu mutane ɗaya ne” 😹.
Ka ajiye wannan ma a gefe…
Yau kusan shekara 4 kenan da Elon Musk ya sayi X akan Dollar Billion 44 😭.
Wato kuɗin da zai iya sa Najeriya ta daina cewa “network busy” na wasu shekaru 😂.
Abun mamaki ma ba nan yake ba…
Transfer charges kaɗai da bankuna suka samu wajen tafiyar kuɗin, sun kai kusan Million 200 Dollars 😭.
Wato kamar yadda Opay zai cire maka ₦10 idan ka tura ₦500… amma wannan karon ₦297 Billion aka cire 😹.
Ka san me wannan yake nufi kuwa?
₦297 Billion ɗin nan kusan ya yi daidai da budget ɗin wasu jihohi 😭.
Kai kuma har yanzu idan aka cire maka ₦50 transfer charges sai ka duba balance sau 3 😭😂.
Wallahi wannan rayuwar tana koya mana humility 😹.
Shi yasa nake cewa:
Ka rage girman kai, ka bi Allah sau da ƙafa 😭🙏.
Domin a gaskiya…
Mu da kai har yanzu “kuɗin cefane” muke ta fama da shi 😂.
post-image
Trang này có thể chứa nội dung của bên thứ ba, được cung cấp chỉ nhằm mục đích thông tin (không phải là tuyên bố/bảo đảm) và không được coi là sự chứng thực cho quan điểm của Gate hoặc là lời khuyên về tài chính hoặc chuyên môn. Xem Tuyên bố từ chối trách nhiệm để biết chi tiết.
  • Phần thưởng
  • Bình luận
  • Đăng lại
  • Retweed
Bình luận
Thêm một bình luận
Thêm một bình luận
Không có bình luận
  • Đã ghim